fbpx
Friday, January 21
Shadow

Hukumar tace fina-finan Kano ta hana dora fina-finan Kannywood da ba a tace ba a YouTube

Hukumar tace fina-finai da dab’iu ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce daga yanzu babu wani fim mai dogon zango da za ta bari a dora a Youtube ba tare da an kai mata ta tace shi ba.

Shugaban hukumar, Isma’il Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun dauki matakin ne sakamakon yadda ake sakin wasu fina-finai da suka ci karo da al’adu da addinin mutunen jihar ta Kano.

“Muna magane ne a kan yadda sakin fina-finai ya zama ruwan-dare a manhajar YouTube wanda kuma yake zama illa ga tarbiyya..kuma dole ne mu dauki mataki a kan harkar nan ta fina-finai da wakoki da abubuwan da suka shafi dangogin rubuce-rubuce,” in ji shi.

Afakallah ya kara da cewa matakin da suka dauka ya hada da duk wani fim mai dogon zango da za a dauka a wasu wurare amma daga bisani a kai jihar ta Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *