fbpx
Friday, April 23
Shadow

Hukumar tsaro ta Civil Defense ta lalata haramtacciyar matatar mai tare da kame wasu mutane 6 da ake zargi a Jihar Delta

Hukumar tsaro dake baiwa farar hula kariya (Civil Defense) ta ce ta rusa wani sansani haramtacciyar matatar mai tare da kame wasu mutane shida da ake zargi a wasu sansanoni a Olokpobiri, da ke yankin Warri South-West na jihar Delta.

Kwamandan NSCDC na jihar, Chike Ikpeamonwu, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a Asaba, babban birnin jihar, ya ce wadanda ake zargin suna tsakanin shekaru 18 zuwa 30.

Mista Ikpeamonwu ya ce ayyukan barayin suna da tasirin wajen koma bayan tattalin arziki da kiwon lafiya, yana mai cewa an dukufa wajen cafke masu gudanar da wannan aikin ba bisa ka’ida ba.

Kwamandan ya kara da cewa samamen a sansanonin Kanto da ke Olokpobiri Warri Kudu maso Yamma na daya daga cikin kokarin da ake yi na ganin an kare muhimman ababen more rayuwa da habaka tattalin kasa daga durkushewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *