fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta cafke tirela 2 dauke da buhunan masara da ta lalace

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCAC) ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da alaka da tirelolin guda biyu dauke da lalatattar masara mai guba a kasuwar Dawanu da ke jihar.

Kasuwar Dawanau ita ce mafi girma a yammacin Afirka, inda ake sayar da hatsi iri -iri kuma tana cikin tsohon birnin Kano.

Mukaddashin Shugaban zartarwa, PCAC, Barr. Mahmoud Balarabe, ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske jim kadan bayan rufe shagon da ake ajiye kayan a Kano a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba.

A cewar Balarabe, a ranar 16 ga Satumba, da misalin karfe 8:00 na dare, hukumar ta samu rahoton leken asiri cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun shigo da lalatattar masara mai guba a kasuwar kayan abinci na Dawanau, Kano.

Bayan samun bayanan, nan take suka isa wurin tare da yan sanda domin kama wadanda ake zargin tare da rufe dakunan aje abincin.

Hakama, ya yi ishara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya kara da cewa hukumar ba za ta bar duk wanda ke da hannu a cikin irin wannan aika -aikar.

A cewarsa, hukumar za ta gayyaci shugabannin kasuwar Dawanau musamman wadanda ke kula da masara, gero don gano ko sun san wani abu game da wannan danyen aiki.

Daya daga cikin wadanda ake zargi, Musa Ibrahim, ya ce “Ban san komai game da wannan lamarin ba, an kama ni lokacin da abokina” Maigari “ya ce in raka shi zuwa shagonsa da ke kasuwar Dawanau.”

Ibrahim ya kuma bayyana cewa kayayyakin da aka kama na abokinsa ne, Adamu Maigari wanda ke sayar da masara tsawon shekaru 15 da suka gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *