fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Hukumar yan karota a Kano ta kama wata mota dauke da tabar wiwi

Hukumar kula da zirga -zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta ce ta kama wata mota dauke da tabar wiwi a cikin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Nabilusi Abubakar, ya rabawa manema labarai ranar Alhamis a Kano.

A cewar sanarwar, “an boye tabar wiwin a cikin wata motar Golf mai lamba: SMK 904 XV, wanda wani Abubakar Aminu mazaunin Sabon Titi Gidan Kankara a jihar Kano ya tuka.

Manajan Daraktan Hukumar, Dakta Baffa Babba-Dan’agundi, ya mika kayan da aka kwace ga hukumar NDLEA, Kano Command.

Ya gargadi ma’aikatan KAROTA da su tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su shigo jihar da haramtattun kwayoyi ko abubuwa masu hadari ga lafiyar dan adam da rayuka ba.

Manajan Daraktan ya yi kira ga sauran jama’a da kada su yi kasa a gwiwa wajen tallafawa hukumar ta hanyar samar mata da sahihan bayanai da za su kai ga cafke masu laifi.

Ya sake nanata cewa koyaushe akwai kyauta ta musamman ga irin wannan aiki.

Babba-Dan’agundi ya kuma tabbatar wa Shugaban NDLEA goyon bayan hukumar da karin hadin kai a yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar.

Kwamandan NDLEA, Mista Isah Likita, ya jinjinawa KAROTA kan kamun yana mai cewa dole ne dukkan hannaye su kasance cikin shiri don yakar shan muggan kwayoyi.

Ya ce yana da mahimmanci mutane su fahimci cewa yakin na kowa ne wanda dole ne duk wani mai ruwa da tsaki ya shiga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *