fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta talauce, bata da kudin gudanar da ayyuka>>IGP

Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya bayyana cewa, Hukumar tasu bata da kudin gudanar da ayyuka duk da tashin tashinar da ake fama da ita a Najeriya.

 

Yace saboda rashin kudin, a yanzu sun koma addu’a ne kawai. Yayin da ake ta kai musu hare-hare.

 

Ya bayyana cewa babu abinda mutum zai iya yi idan ba da kudi ba, dan hakane ma yake kira ga majalisa da ta taimaka ta duba wannan lamari.

 

Ya bayyana hakane a ganawarsa da Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *