fbpx
Monday, November 29
Shadow

Idan Buhari da gaske yake kan magance matsalar tsaron Najeriya, harin Auno ya kamata ya sashi ya yake ziyarar da yake ya dawo gida>>Jafar Jafar

Tauraron dan Jarida, mawallafin Jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar yayi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa idan dai da gaske yake akan magance matsalar tsaro ya kamata ace ya yanke ziyarar da yake a kasar Ethiopia ya dawo gida Najeriya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A ranar Lahadi ne Boko Haram ta kai hari a garin Auno dake daf da babban birnin jihar Borno, Maiduguri inda rahotanni suka bayyana cewa sun kashe mutane 30 tare da cika motoci da mata da yara suka yi awon gaba dasu.

A martaninshi ga wannan lqmari, Jafar Jafar ya runuta a shafinshi na dandalin Twitter cewa idan dai shugaba Buhari da gaske yake kan maganin matsalar tsaro to harin Auno ya kamata yasa shi yanke ziyarar da yake a kasar Ethiopia ya dawo ya fuskanci matsalar mu ta cikin gida dan harin yafi matsalar kasar Libya.

Shugaba Buhari a wajan taron na kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta AU yayi Allah wadai da masu ruruta wutar rikicin kasar Libya.

A watan Disambar shekarar data gabata, shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya yanke ziyarar da yake a kasar Egypt ta taron tsaron nahijar Africa da aka tara shuwagabanni daban-daban inda ya koma kasarshi Nijar saboda harin da ‘yan ta’adda suka kaiwa sojojin kasar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *