fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Idan da Obasanjo ko Jonathan ke jagorantar Najeriya, ba su yarda da irin sukar da ake yi wa Buhari dake kan mulki ba- Ngige

Chris Ngige, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya ce babu wani shugaban kasar da zai yarda da abin da ‘yan Najeriya ke jefawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ngige ya ce ‘yan Najeriya na ganin Buhari a matsayin “dokin yarda” da za a hau zuwa mutuwa.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels, Ministan ya yi ikirarin cewa tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan ba za su amince da wasu suka da ake yi wa Buhari ba.

Ya kuma yi watsi da ikirarin da ake yi cewa Buhari na kaunar karya doka.

Ngige ya ce Shugaban kasar na tsoron keta dokar Najeriya.

Ya ce: “Idan wata gwamnati ta yi kyau; idan shugaban kasa ya yi kyau, ba shi yabo a can. Yankunan da bai tabuka abin kirki ba, nuna musu su tattauna.

Buhari dan dimokiradiyya ne kuma yana matukar tsoron sabawa tsarin mulki ko wata doka. Na ma fi shi ƙarfi dangane da hakan.

”Ko Shugaba Obasanjo, zai iya ba ku wannan damar? Ba zai yi ba. Na san shi. Ko tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai kyale irin wannan ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *