fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Idan fa aka raba Najeriya, Farfesa zai iya komawa yana aikin gidan biredi>>Lai Muhammad

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, manyan mutane da suka kai matsayin Farfesoshi ya kamata su daina Tunzura mutane.

 

Yace yawancin matsalolin daga wajan irin wadannan mutane suke tasowa, yace da zaka je kauyuka. Zaka ga mutane na zaune lafiya duk da banbancin kabila ko addini.

 

Yace amma irin manyan mutane da ya kamata ace suna taimakawa wajan yada akidar Zaman lafiya, idan suka koma yada kiyayya sai abin ya lalace, saboda yawanci mutane suna saurarensu da tunanin cewa sun fisu sanin harkar Rayuwa.

 

Yace irin wadannan mutane suna da fasfo na kasashe da yawa, kuma da an fara wani tashin hakali zasu tsere ne su bar mutane cikin matsala. Yace amma fa su sani zasu iya komawa aikin gidan biredi a kasashe irin su Togo, yace a baya anga irin yanda hakan ta faru yayin da kasar Liberia ke fama da yakin basasa.

 

“The elites will suffer more because some professors could be working in bakeries in Togo just to survive. We saw it happen when the Liberians came here during their civil war.

“It is in their own enlightened interest that they should work to fix Nigeria. Many of them have more than one passport — American, British, Irish — and at the first crack of trouble, they are gone.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *