fbpx
Monday, May 10
Shadow

Idan gwamnatin tarayya ta ki bamu kudi Matsalar Tsaro zata iya Karuwa>>Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, idan gwamnatin tarayya ta ki baiwa Jihohi kudin da ta saba basu duk wata to akwai matsala, dan kuwa rashin tsaro ka iya karuwa.

 

Ya bayyana hakane ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Shugaban ma’aikatan fadar, Farfesa Ibrahim Gambari.

 

Masari yace rashin kudi na daga cikin abinda ke kara yawaitar matsalar tsaro, yace dan sai da kudi ne ake samarwa matasa musamman a yankunan karkara ayyukan yi wanda sune ‘yan bindigar ke jan ra’ayinsu shiga wannan mummunar hanya.

 

Masarin na martanine ga kamfanin mai na kasa, NNPC da ya bayyana cewa, an samu karancin kudi kuma wata kila kudaden da za’a turawa jijohi a Watan Mayu su ragu.

“Without resources, again, it’s another factor that affects security, you cannot create jobs for the teeming unemployed youths in the rural communities…It’s with resources state governments and local governments we’ll be able to contain some of these restive youths so that they can be used for better purposes because most of them might be foot soldiers to the bandits.” Daily Trust.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *