fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Idan matasan Najeriya na son samun aikin yi to su nutsu su daina tada hankula>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa matasan Najeriya shawarar su nutsu su daina kawo tashin-tashina inda suna son sam7n aik8n yi.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace babu wanda zai kawo dukiyarsa ya zuba a Najeriya idan babu tsaro.

 

Yace dan haka matasa su nutsu su daina tada fitina, ko kamfanonin kasashen waje zasu ga damar zuba jari a Najeriya.

Yace lallai Najeriya Allah ya albarkaceta da albarkar kasa, amma maganar rashin zaman lafiya ne ke kawo mata cikas.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *