fbpx
Monday, November 29
Shadow

Idan Najeriya ta bari aka sake sace kudin Abacha sai ta biya>>Amurka

Gwamnatin Amurka ta shardanta wa Najeriya cewa muddin ta bari aka sace kudin da take shirin dawo mata da su yayin aikin da aka tsara za a gudanar da su to sai ta biya.

A ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Amurka ta shardanta cewa Najeriya za ta biya duk wani kudi da aka sace yayin gudanar da aiyukan raya kasa da aka karbo kudin dominsu, kamar yadda suka yi yarjejeniya.
Gwamnatin Najeriya ce ta wallafa wannan sanarwar a shafinta na Twitter a ranar Talata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ranar Lahadi ne Ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami, ya je birnin Washington na Amurka domin saka hannu kan yarjejeniyar dawo da kudin da tsohon shugaban mulkin soji Sani Abacha ya sace kuma ya jibge su a can.

Kudin sun kai dalar Amurka miliyan 308, kwatankwacin kusan naira biliyan 112.

“Hukumar kula da asusun zuba jarin kasashen waje a Najeriya (Nigeria Sovereign Investment Authority) za ta yi amfani da su ne wurin yin manyan aiyukan raya kasa a bangarorin tattalin arziki uku na Najeriya, in ji sanarwar.

“Domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudin yadda ya kamata, yarjejeniyar ta tsara yadda za a gudanar da aiyukan sannan kuma ta bukaci Najeriya ta biya duk wani kudi da aka sace yayin gudanar da aiyukan da aka karbo kudin dominsu.”

Amurka ta ce wannan yunkuri ya nuna irin kokarin da take yi na yaki da cin hanci da rashawa a kasashen duniya sannan kuma bangare ne na wata yarjejeniyar da Najeriya ta cimma da Amurkar da kuma Birtaniya a taron 2017 Global Forum on Asset Recovery.

A karshe kuma ta yaba wa Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari game da yunkurin da gwamnatinsa ke yi na dawo da kudaden da aka sace daga kasar zuwa lalitarta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *