fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Idris Abdulkarim ya mayarwa sa Minista, Festus Keyamo martani

Tauraron mawaki, Idris Abdulkarim da ya sake yin wakar Najeriya Jaga-Jaga, karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ya fallasa cewa ya nemi ya bashi kudi a sekarar 2018 amma ya kiya ne, shiyasa ma ya sakashi a cikin wakar tashi.

 

Saidai a martanin Idris, yace a wancan lokacin mahaifiyarsa na fama da rashin lafiyane shine ya nemi Keyamo ya taimaka masa kuma zai iya taimaka masa din amma yaki.

 

Yacs Keyamo ya manta lokacin Obasanjo da aka kulleshi a gidan yari, shi kuma ya rika fafatawa da gwamnatin Obasanjo a wancan lokacin kan sako duk wanda ake tsare dasu.

 

Yace amma yanzu Keyamo ya koma cikin wanda ake muzgunawa mutane tare dashi ya daina fafutukar kare jama’a. Yace, yacs burinsa nan gaba Shine ya fito takarar gwamnan jihar Delta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *