fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

IG ya bada umarnin tsaurara matakan tsaro kafin bikin Sallah ta Eid-el-Kabir

Sufeto janar na ‘yan sanda (IGP) Usman Alkali Baba ya umarci Mataimakan Sufeto-janar na’ yan sanda (AIGs) da Kwamishinonin ‘yan sanda (CPs) da su sanya matakan tsaro da suka dace don tabbatar da cewa anyi shagulgulan bikin Sallah a cikin kwanciyar hankali, lumana da walwala.

Baba ya tabbatar wa kasar cewa ‘yan sanda a shirye suke su ci gaba da kokarin yaki da aikata laifuka tare da inganta tsaro a fadin kasar.

A wata sanarwa da aka fitar jiya a Abuja ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba, wani kwamishinan ‘yan sanda (CP), ya ce:“ IGP din ya ba da umurni ga Zonal AIGs da Kwamandojin Jihohi da su sanya duk matakan tsaro da suka dace don tabbatar da tsaro domin ayi bikin cikin lumana da walwala.

A karshe IG yayi kira ga jama’a da su zama masu bin doka da oda a lokacin bukukuwan Sallah tare da kai rahoton duk wani abu da basu aminta da shi ba ga hukumar yan sanda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *