fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

Ighalo zai buga wa Man United wasanta da Chelsea

Odion Ighalo yana cikin ‘yan wasan da za su fuskanci Chelsea a gasar Premier ranar Litinin in ji Ole Gunnar Solskjaer.

Ighalo bai je wasannin atisaye da United ta yi a Spaniya ba, sakamakon tsoron yada coronavirus dalilin da aka hana shi takardar izinin shiga kasar.
Dan kwallon tawagar Najeriya, mai shekara 30 ya koma Old Trafford da taka leda aro daga 


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Tsohon dan kwallon Watford ya koma buga gasar China a 2017, inda ya fara da kungiyar Changchun Yatai.

Bayan da ya buga kaka biyu sai ya koma Shanghai Shenhua wadda ya buga wa wasa 19 ya kuma ci kwallo 10.

Ighalo ya taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda ya ci kwallo bakwai, kuma ya zura biyar a wasannin neman gurbin shiga gasar.

Rabon da Ighalo ya buga kwallo tun 6 ga watan Disamba a lokacin da ya canji dan wasa a karawar da Shanghai Shenhua ta doke Shandong Luneng 3-0 a gasar FA Cup ta China.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *