fbpx
Monday, September 27
Shadow

IN DAI MUTANEN BANZA NE KADAI SUKE YIN RASHIN LAFIYA DA CUTAR CANCER BA ZATA KASHE ALI BANAT BA

DAGA Gen Sunus, Bulaliya

Tun lokacin aka samu labarin Jaruma Maryam Yahaya bata da lafiya duk da har yanzu an rasa wanda zai fito ya fadi ainihin cutar da take damunta amma da yake wasu mutanen sun mayarda kansu jakadun Bala’i kowa yazo yana Shaci Fadi lallai sai ya fadi menene yake damunta. Duk da wasu yan film din suke janyowa kansu matsala.

Meyasa a lokacin da matashin nan mai taimakawa al’umma musamman marasa lafiya wato Ali Banat” dan kasar Australia yayi ciwon Cancer ya mutu babu wanda ya danganta ciwonsa a matsayin izina ga ayyukan alkhairin da yake yi, Ko don saboda shi ba ɗan film bane.

Don Allah Ustazai nawa kasani sun taɓa haduwa da matsala amma hakan bai zama labari ba sai akan ƴan film duk abinda ya samesu sai an dangantashi da sana’arsu ance izina ce. Maimakon ayi musu addu’ar samun lafiya kuma a jira aji ainihin gaskiyar abinda yake damunsu.

Nace dama wai mutanen banza ne kadai suke rashin lafiya kuma idan sunyi rashin lafiya kuma hakan yanada alaqa da ayyukansu, Idan kuwa hakane su kuma Malamai da sauran Salihan Bayi da suke yin rashin lafiya shin hakan yanada alaqa da ayyukansu nagari kenan ko kuma Ubangiji zai iya jarrabar kowa da ciwo?

Allah ya bawa Maryam Yahaya Lafiya Tare Da Dukkan Musulmai…!

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *