fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ina da ‘yan Uwa a Kasar Nijar>>Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayin da aka tambayeshi kan maganar gina titin jirgin kasa zuwa Nijar

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yana da ‘yan uwa a kasar Nijar. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV.

 

An tambayeshi dalilin da yasa ake gina titin jirgin kasa zuwa kasar Nijar, Shugaban ya kayar da baki yace ya kamata muna da kykkyawar alaka da makwabtan kasashe.

 

Shugaba Buhari yace akwai Fulani da Kanuri da Hausawa a Nijar, kamar yanda akwai Yarbawa a Benin.

 

Yace bai kamata ba kuma a yankesu daga Najeriya ba, Shugaban ya kara da cewa, Nijar ta gano man fetur kwanannan, yace suna son ta rika bi ta Najeriya idan zata fitar da kayanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *