fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ina ganin Girman Buhari a Idona>>Buba Galadima

A hirarsa da BBChausa, Shahararren dan Siyasa, Buba Galadima ya bayyana yanda alakarsu ta fara da shugaban kasa, Muhammadu Buhari tun yana gwamnan Borno.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A cewar Buba Galadima kasancewarsa mai ra’ayi a kan duk wani batu ne ya sa ba shi da farin jini wajen shugabanni a Najeriya.

Ya kara da cewa “Dukkan mutumin da ba zai kwantar da kai idan an ce masa Allah 10 ne ya ce eh ba, toh ba zai samu farin jini a wajen shugabanni irin na Najeriya ba.”

Buba Galadima ya bayyana cewa “an tuhume ni ko kulle ni ko ja mani kunne ko an sa mani ankwa an sa ni a karkashin kasa sau 38.”

Ya ce an fara kulle shi a 1984 a zamanin mulkin soja na Shugaba Buhari.

‘Alakata da Buhari’
Buhari na daya daga cikin mutanen da nake ganin girmansu a ido na.

Mun fara mu’amala da shi tun yana gwamnan Borno, amma “shi ba zai iya tunawa ba amma ni da yake ina karamin jami’i zan iya tunawa.”

Buba Galadima ya ce sun fara harkar siyasa da Buhari tun shekarar 2002 bayan Buharin ya shiga jam’iyyar APP a lokacin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *