fbpx
Monday, October 25
Shadow

Ina mamakin shugabanni da ke canza tsarin mulki don ci gaba da mulki – Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa da rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da yin ta’adi da kundin tsarin mulki na wasu shugabannin kasashen Afirka don tsawaita wa’adin mulkinsu.

Wannan shi ne kamar yadda ya ce ya kamata a yi zabe lafiya da kwanciyar hankali, ba tare da tursasawa ta kowace hanya ba.

Buhari ya fadi haka ne a ranar Juma’a yayin wata ganawa ta hadin gwiwa da wakilin dindindin na Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Shugaba Buhari ya yaba da tallafin da Amurka ke bayarwa kan yaki da ta’addanci.’

Tun da farko, Jakadiyar ta lura cewa kusan kashi 70% na ayyukan ta a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya kan Afirka ne, kuma ta nuna damuwa game da karbe ikon mulki da sojoji suka yi kwanan nan a Mali da Guinea.

A martanin da ya mayar, Buhari ya ce dole ne shugabanni su girmama mutanen su, wanda daga ciki akwai yin biyayya ga sharuddan takaita mulki a cikin Tsarin Mulkin su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *