fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Ina sane da bakar wahalar da ‘yan Najeriya ke sha>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yana sane da wahalar da ‘yan Najeriya ke sha.

 

Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a Channels TV.

 

A hirar da aka yi dashi ranar Laraba a gidan talabijin din, shugaban yace yana sane da wahalar da mutane ke yi wajan samun abinci.

 

Shugaban yace amma ga kasa nan da Allah ya wadata Najeriya da ita kuma kaso 2.5 cikin 100 ne na kasar kawai ake nomawa.

 

Yace mafita itace a koma gona.

Leave a Reply

Your email address will not be published.