fbpx
Monday, September 27
Shadow

Ina so a rika tunawa da ni a matsayin wanda ya daidaita Najeriya>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad ya ce yana so a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya daidaita Najeriya ta fuskar tsaro da tattalin arziki da habbakar kasa da nasarar da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a Owerri ranar Alhamis.

Shugaban ya bayyana wa shugabannin kudu maso gabashin Najeriya a wata ziyara da ya kai ta kwana guda a jihar Imo cewa, cikin abin da ya yi kasa da shekara biyu da ya rage na mulkinsa, har yanzu harkar tsaro ita ce abin da ya fi bai wa mahimmanci.

Quote Message: Idan babu tsaro, babu wanda ya isa ya yi wani abu, duk yadda za a yi kokarin kawo ci gaba. Tsaro shi ne abu mafi mahimmanci sannan tattalin arziki. Lokacin da mutane ke da cikakkiyar nutsuwa kan harkar tsaro ko wa zai mayar da hankali kan abin da yake gabansa..in ji Buhari.

Shugaban ya ce lokacin da yaki da cin hanci ke kara zama abu mai wuya a Najeriya, yana son ya bar wani tarihi da bajinta da za a rika tunawa da shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *