fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ina tare da Rarara kan cewa a karawa Buhari wa’adin Mulki amma mutanen mu sun dauka Buharine matsalar rayuwarsu>>Datti Assalafy

SHUGABA BUHARI ALHERI NE GAREMU

Na saurari hiran da BBC tayi da abokina Dauda Adamu Kahutu (Rarara) suka tambyeshi ko idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa zai dena waka? ya amsa da cewa lokaci ne zai nuna

Rarara yace a ra’ayinsa yana zo a karawa shugaba Buhari lokaci kamar shekara 4 ko 5 saboda ya kara ayyukan alheri da ya fara, yace amma ba kowa zai fahimci alherin hakan ba saiga wanda yasan me Shugaba Buhari yakeyi a kasa

Maganar da Rarara ya fada gaskiya ne, amma mutanen mu sun dauki dukkan damuwarsu da matsalarsu sun daura akan shugaba Buhari, suna ganin kamar shine ya kawo musu damuwa da matsala, don haka ya tafi kawai

Shugaba Muhammadu Buhari ba shine matsalar mu ba, bamu taba yin shugaba a mulkin Demokaradiyyah wanda yake son mu kamar shugaba Buhari ba

Zamu ga amfanin shugaba Buhari idan wa’adin mulkinsa ya kare, lokaci zai zama alkali a tsakanin mu da masu zagin shugaba Buhari

Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Ka bashi ikon kammala mulkinsa lafiya Amin

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *