fbpx
Saturday, October 16
Shadow

INNA LILLAHI WA’INNA ILAHI RAJI’UN: Mu Dai Dauke ‘Network’ A Yankinmu Musiba Ya Zane Mana

Daga Lukman Gambo S/Bilbis

Wannan dauke Network da aka yi a yankinmu babu wani abu da ya haifar mana face Kara jefa mu cikin musifa, bala’i da tashin hankali.

An dauke mana network an kulle mu a wani loko ana tayi mana kisan mummuke ba tare da kowa ya sani ba.

A baya mun sha wahala a hannun ‘yan ta’adda amma ba mu kara shiga cikin matsanancin tashin hankali ba sai yanzu bayan an dauke mana network.

Tun daga ranar da aka ce an dauke network din Zamfara wanda shine ya hada da Kauyukanmu na Katsina wadanda muke makwaftaka da Zamfara Wallahi babu ranar da ‘yan ta’adda basa shiga garuruwanmu suna yi mana ta’asa.

A Kasa da sati daya ‘yan ta’adda sun shiga garinmu na S/Bilbis sama da sau biyar (5) sun dauki mutane da yawa, wasu an biya kudin fansa wasu kuma suna hannunsu.

A ranar Lahadi data gabata 26/09/2021 da yamma sun shigo bakin garin namu sun bude wuta kan mai uwa da wabi wanda sai da yayi sanadiyyar kashe mana zunzurutun matasa har guda uku (3) tare da jikkata wasu da dama wanda yanzu haka suna asibiti.

Ya Ilahil Alamina mu yanzu ina zamu saka kanmu? An kashe mana mutane bila adadin, an jikkata wasu, wasu kuma suna hannunsu a cikin daji, gashi kuma amfanin gonar da mutane suka shuka ya isa girba amma kowa na tsoron zuwa gona ya girba domin ta ko ina ‘yan ta’adda ne a kewaye damu.

Kuma kullum mahukunta suna karyar cewa an dauke Network ana aiki akan ‘yan ta’adda amma Wallahi Karya suke, domin a yankin namu babu soja ko guda daya balantana dan sanda babu abunda Jami’an tsaron ke yi a wajen, ‘yan ta’addan ne kawai ke cin karensu babu babbaka a kowanne lokaci.

Zaman dar-dar, fargaba da zullumi shine kullum iyayenmu da Yan uwanmu suke yi, kowa ya fita hayyacinsa saboda tsabagen tashin hankali, Wanda bai isa furfura ba farin gashi duk ya tsire masa a kansa saboda fargaba da tsoro, ga yunwa da talauci sun yiwa jama’a katutu.

A gaskiya dole ne mufadi cewa gwamnati ta kasa saboda irin abubuwan da akeyi mana a kauyukanmu. Kuma a madadin duka garin namu da makwabta muna fatan Allah yasa gomnati taga wannan rubutu kuma takawo mana agaji.

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Rajiuun 😭😭😭

Ya Allah Ka kawo mana taimakonKa da agajinKa ta inda muke zato da inda bama zato, Ya Allah ba dan halinmu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *