fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Inyamurai na ta tofin Allah tsine kan IPOB

Kashe mijin Dora Akunyili da ake zargin IPOB da yi ya jawowa kungiyar bakin Jini a wajan Inyamurai da yawa.

 

An dai kashe Chike Akunyili ne akan titi inda aka ga gawarsa na ta jawo a shafuan sada zumunta.

 

Saidai IPOB ta nesanta kanta da kisan inda tace kisan siyasa ne amma bata da hannu a ciki.

 

Saidai duk da haka, inyamurai da dama a shafukan sada zumunta na yanar gizo na ta Allah wadai da kungiyar inda suke cewa ta fara wuce makadi da rawa.

 

Misali, wani me sunan Ikenga Okija ya bayyana cewa, IPOB ta rasa alkibla, ku yi abu amma ku rika karyatawa ba zai kaiku ko ina ba.

 

Shima wani me suna Ediong ya bayyana cewa, amincewa da ayyukan IPOB a kudu, kamar shan gubane amma kuma mutum ya yaudari kansa da cewa ruwane ya sha.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *