fbpx
Sunday, September 26
Shadow

IPOB ba su da bambanci da ISWAP, Boko Haram – Gbajabiamila

 

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya kwatanta kungiyoyin ‘yan aware na kudancin kasar nan da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabas; Boko-Haram da ISWAP.

Mista Gbajabiamila ya ce bata gari da ke fakewa da kungiyoyi masu neman ballewa ba su da hakuri shi ya sa suka mayar da kansu kamar kungiyoyin masu zubar da jini a arewa maso gabas.

Ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta sanya kungiyar IPOB cikin jerin wadannan kungiyoyi.

A cewar Kakakin, “A Kudancin Najeriya, Gabas da Yamma, miyagun mutane da masu aikata laifuka da ke fakewa da masu fafutukar rabuwa sun bullo don yin barna, kashe rayuka da yin zagon kasa ga‘ yan Najeriya.

Ya kara cewa Gwamnatin Najeriya za ta yi duk abunda ya dace domin ganin an kawo karshen rashin tsaro a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *