fbpx
Monday, September 27
Shadow

IPOB sun shigar da kasar Amurka kara a kotu kan sayarwa da Najeriya makamai

Haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, ta roki kasar Amurka da ta daina sayarwa da Najeriya jiragen yaki kirar Super Tucano.

 

Hakanan abin bai tsaya akan roko ba, IPOB ta kuma maka kasar ta Amurka a Kotu inda take neman a dakatar da aikawa Najeriya jiragen yaki 6 da aka kera mata, sannan kuma a karbo 6 da aka riga aka kawo Najeriya.

 

Lauyan IPOB a kasar Amurka, Bruce Fein ne ya shigar da karar a madadin IPOB, inda suke karar Sakataren harkokin kasar waje na Amurkar, Anthony Blinken da kuma sakataren tsaro na kasar Lloyd Austin da sauran wasu jami’an gwamnatin kasar.

 

IPOB ta bayar da dalilin cewa wai itace za’a kaiwa hari da makaman shiyasa bata son a sayarwa da Gwamnatin Najeriya su.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *