fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

IPOB ta bayar da umarnin cire tutar Najeriya a Jihohin Inyamurai kuma bankuna sun bi umarnin

Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin cire tutar Najeriya a Jihohin Inyamurai saboda bikin ranar ‘yancin kan Najeriya.

 

Ranar 1 ga watan October ne Najeriya ta samu ‘yancin kai, kuma duk idan wanan rana ta zagayo akan yi bikin tunawa da ranar ‘yanci.

 

Saidai kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra tace a cire tutar Najeriya a yankunan jihohin Inyamurai.

 

Wani abu da ya dauki hankula shine yanda aka ga bankuna sun bi wannan umarni.

 

Bankunan Access, Wema, UBA da sauransu ne suka bi umarnin IPOB din.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *