fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

IPOB ta yi tir da shawarar da Miyetti Allah ta yanke na tura ‘yan banga 5000 zuwa yankin Kudu maso Gabas

Kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra IPOB da aka haramta sun yi tir da shirin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria na tura’ yan banga 5,000 zuwa yankin Kudu maso Gabas.

Kungiyar Miyetti Allah a kwanan nan ta sanar da cewa za ta tura ‘yan banga don kare makiyaya da shanunsu a Kudu maso Gabas.

Sai dai a cikin wata sanarwa da Daraktan ta na yada labarai, Emma Powerful ya fitar, IPOB ta ce a shirye ta ke ta bijire wa shirin na Miyetti Allah, inda ta kara da cewa matsayin kungiyar makiyayan shanun cin fuska ne a kasar ta Igbo.

Ya kuma ce, ya kamata kungiyar Miyetti Allah da kungiyar ‘yan ta’addansu su san cewa bai kamata su yi wasa da Allah ba har abada.

Ya kara da cewa kungiyar Miyetti Allah suna kokarin harzuka ESN da IPOB don daukar tsauraran matakai.

Amma IPOB da ESN hakuri su ya fara karewa domin kuwa ba zasu jure duk wani yunkuri ko cin zarafi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *