fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Iran: Amurka ba ta ga komai ba tukunna

Kakakin Rundunar Sojin Iran Birgediya Janar Abulfazli Shikarchi ya bayyana cewar ba sa kallon harin da suka kai sansanonin Amurka a matsayin “ramuwar gayya”.

Sanarwar da Shirkachi ya aikewa da kamfanin dillancin labarai na Fars ta ce  a su ci gaba da zama a yankin har sai lokacinda Amurka ta kwashe sojojinta daga gabas ta tsakiya.
Shirkachi ya ci gaba da cewar Amurka ba ta da garkuwar makamai masu linzami mai inganci domin ta gaza kawar da hare-haren da suka kai kan sansaninta, kuma wannan abu darasi ne ga kasashen da suke aiki tare da Amurka.
Ya ce “Harin da muka kai wa Amurka a Iraki ba mu dauke shi ramuwar gayya ba. Ramuwar gayyar da za mu yi Amurka za ta sanya su tattara nasu i nasu su bar yankin.”
Da yake mayar da martani game da cewar Iran da Amurka sun tattauna kafin a kai harin wanda hakan ya sanya suka bar wajen, sai ya ce “Wannan karya ce mai bayar da dariya. A tarbiyyance wannan kamar yana cin karo da kutufar abokin gaba. Muna kallon Amurka a matsayin makiya kuma mai kisan gilla. Amurka ce take kirkirar wannan karya don cimma manufarta.”
Kakakin Rundunar Sojin ta Iran ya kuma karyata cewar an yi amfani da makamai masu linzami wajen harbo jirgin saman Yukren da ya fado a Tehran, wannan wani yaki ne da kwakwalwa da ake yi don kare manufofin Amurka.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *