fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

‘Iran ce ta harbo jirgin Ukraine bisa kuskure’>>Inji Kasar Amurka


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kasar Iran ce ta harbo jirgin saman Ukraine mai dauke da mutum 176 bisa kuskure, a cewar wasu kafofin yada labarai a Amurka.

Jami’an Amurka sun ce sun yi imanin cewa jirgin na Ukraine kirar Boeing 737-800 an harbo shi ne da makami mai linzami, kamar yadda kafar yada labarai ta CBS ta ce.
Kasar Ukraine ta ce tana bincike kan ko makami mai linzami ne ya harbo jirgin, amma Iran ta ce batun ba haka ba ne.
Jirgin ya fadi ne sa’o’i kadan bayan da Iran ta harba makamai masu linzami a wasu sansanin sojojin Amurka guda biyu a Iraki.
Kafar yada labarai ta CBS ta ruwaito wasu bayan sirri wadanda ke nuna cewa tauraron dan Adam ya ga “barbashin kusantar” makamai masu linzami guda biyu, da kuma barbashin fashewar wani makamin.
Har ila yau, kafar yada labarai ta Newsweek ta ce Ma’aikatar Tsaro ta Amurka wato Pentagon da wani babban jam’in leken asiri da kuma wani jami’in leken asirin Iraki sun yi amannar cewa wani makami mai linzami ne da aka kera a Rasha ne aka yi amfani da shi wajen harbo jirgin.
A ranar Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: “Muna da shakku” dangane da jirgin. “Tana iya yiwuwa wani ya yi kuskure,” in ji shi.
Yayin da ake ci gaba da zaman tankiya tsakanin Iran da Amurka bayan kisan Janar Qasem Soleimani, Iran ta ce ba za ta bai wa kamfanin Boeing (wanda ya kera jirgin) ko kasar Amurka na’urar tattara bayanai ta (Black Box) ba.
Kamar yadda dokokin sufurin jirgin sama na duniya ta tanada, Iran tana da damar jagorantar binciken abin da ya jawo hadarin jirgin, sai dai za ta yi hakan ne da hadin gwiwar kamfanin da ya kera jirgin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *