fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Irin shugabancin da Najeriya ke bukata – Atiku Abubakar

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana irin shugabancin da Najeriya ke bukata gabanin zaben 2023.

Atiku ya ce Najeriya na bukatar shugabancin da zai kawo hadin kai a kasar baki daya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana fatan kasar nan za ta ci gaba a karkashin jagorancin da zai hada kai da samar da zaman lafiya.

Yayi Magana ne a lacca ta cika shekaru 70 na Engr. Raymond Aleogho Dokpesi, tare da taken: “Fasahar: Hanyar da ta ɓace a Ci gaban Najeriya,” a ranar Alhamis.

Atiku ya jaddada cewa Najeriya na bukatar shugaban da zai gyara kasar da kuma gyara tattalin arzikin kasar.

A cewarsa: “Najeriya na bukatar shugabancin da zai iya hada kan kasa, samar da zaman lafiya, gyara kasa, gyara tattalin arziki da samar da hadin kai ga al’umma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *