fbpx
Monday, September 27
Shadow

Iyalan Sarkin Kajuru 7 sun sami ‘yanci bayan watanni 2 tsare a hannun masu garkuwa da mutane

Iyalan sarkin Kajuru bakwai, Alhaji Alhassan Adamu sun sake samun ‘yanci bayan watanni biyu a tsare.

Idan baku manta ba, ‘Yan bindiga sun sace sarkin da iyalansa a ranar 11 ga watan Yuli, 2021, Amma sun saki Sarkin bayan sa’o’i 24 da sace shi.

Aminiya ta ruwaito cewa wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da mata uku, maza uku da jariri, an sako su ranar Laraba 8 ga watan Satumba, bayan an biya kudin da ba a bayyana ba a matsayin kudin fansa.

Wani mai rike da sarauta a masarautar, Dan Iyan Kajuru Saidu Musa wanda ya tabbatar da sakin wadanda abin ya shafa, ya ce har yanzu yara da jikokin sarkin suna tsare a hannun yan bindingar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *