fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Jama’a a jihar Zamfara sun yi zanga-zanga, tare da toshe manyan hanyoyi don nuna rashin jindadin su gama da matsalar rashin tsaro

An samu tsaiko a ayyuka a wasu yankunan karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a ranar Alhamis yayin da mazauna garin ke zanga -zangar nuna adawa da ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar yankin sama da shekaru goma.

Zanga-zangar lumana ce domin babu wanda aka kashe kuma ba a wanda yaji rauni.

A cewar wani matafiyi, Alhaji Musa Abdulahi, hanyar da ta hada Gusau babban birnin jihar da kuma Zariya ta kasance an toshe gaba daya sama da sa’o’i biyar saboda fusatattun masu zanga-zangar sun ki bude hanyoyin domin zirga-zirgar jama’a.

Ya kuma bayyana cewa hare-haren ‘yan bindiga da ake kai wa a dukkan al’ummar karamar hukumar da rashin jami’an tsaro a lokacin wadannan hare-haren ne musabbabin zanga-zangar.

Ya kara da cewa “A lokacin da muka bar garin Tsafe da misalin karfe 5:40 na yamma ‘yan zanga-zangar sun tsaya tsayin daka kan cewa ba za su bar babbar hanyar ba har sai jami’an tsaro sun tabbatar musu da cewa sun tunkari ‘yan bindigar da aka ambata tare da tabbatar da tsaron karamar hukumarsu baki daya.

Bayanai daga majiyar sun bayyana cewa akwai mata, yara da tsofaffi cikin masu zanga -zangar daga al’ummomi sama da 15.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara (PPRO), SP Shehu Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya tabbatar wa al’ummar karamar hukumar cewa rundunar tana kara kokari wajen inganta harkar tsaro a yankin.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *