fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Jama’a sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja dan nuna bacin ransu kan matsalar tsaro

Jama’ar garin Kakau na karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja dan Nuna bacin rai kan matsalar tsaro data addabesu.

 

Wani dan shekaru 49, Alhaji Ibrahima Dauda ya bayyana cewa, basa iya bacci saboda yanda barayi suka damesu.

 

Yace ‘yan Bindigar suna dauke musu mutane su rika neman kudi masu yawa, ya kara da cewa, su manoma ne basu da kudi.

 

Itama dai wata Madam Rose Gimba ta bayyana cewa, Kauyawan sun tare hanyar ne dan nuna bacin ransu kan matsalar tsaron, kakar yanda Daily Post ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *