fbpx
Monday, September 27
Shadow

Jama’ar garin sun kashe wani da ake zargi dan bindiga ne a jihar Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Magama a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargin dan bindiga ne.

An tattaro cewa wanda ake zargin, mai suna Baleri, wanda ake ya boye kanshi don siyan wasu magunguna a cikin garin.

Duk da haka, wasu mazauna garin sun gane shi kuma sun far masa, amma a karshe kungiyar ‘yan banga ta cece shi da aka ce sun mika shi ga sojojin da ke sintiri a yankin.

Daga baya an ce an ga gawarsa a kusa da kauyen Kukar Babangida na karamar hukumar guda, amma cikakkun bayanai kan yadda ya mutu a ƙarshe ba su da yawa a lokacin rubuta wannan rahoton.

An tattaro cewa ‘yan uwansa guda uku da suka zo daukar gawarsa don binnewa,  jami’an tsaro sun kama su.

Wannan na zuwa ne yayin da aka dakatar da sabis na sadarwar GSM a wasu kananan hukumomin jihar, ciki har da Jibia.

Sauran kananan hukumomin da ke fama da matsalar “no-network service” sun hada da Faskari, Dandume, Funtua, Malumfashi, Bakori, Dutsin-Ma da Batsari da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *