fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Jami’an Hukumar FRSC sun mayar wa da dangin wani fasinja da ya mutu a hatsarin mota N716,800 da suka tsinta

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta mayar wa da dangin fasinjan da ya mutu N716, 800 da aka samu a wani hatsari da ya faru a jihar Anambra.

Kwamandan sashin a Oraifite, Mista Bamidele Ayanwale, wanda ya mika kudin a ranar Talata, 6 ga Afrilu, ya ce an gano kudaden ne a lokacin da jami’an FRSC ke aikin ceto bayan hatsarin.

Ayanwale ya ce hatsarin wanda ya hada da motar Nissan mai lamba LSH-517YG da kuma wata babbar mota mai lamba GGU-83XA, ta faru ne a ranar 22 ga watan Maris, a Ozubulu da ke karamar hukumar Ekwusigo ta jihar Anambara.

Ya ce an mayar da kudin kudin na marigayiya Mrs Oparaocha, ga danta mai suna Mista Chibueze Oparaocha bayan an bayar da gamsasun hujjoji a rubuce.

A nasa bangaren, Chibueze Oparaocha, dan marigayin, ya gode wa FRSC bisa wannan karamci da gaskiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *