fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Jami’an NSCDC sun cafke wani mutum mai shekaru 35 a kan zargin yiwa yarinya ‘yar shekara 5 fyade a Kebbi

Jami’an tsaron dake ba farar hula kariya (NSCDC) sun damke wani matashi mai shekaru 35 a jihar Kebbi bisa zargin lalata wata yarinya ‘yar shekara biyar.

Da yake bayyana hakan ga manema labarai, kwamandan NSCDC a jihar, Umar Musa-Bala, ya ce an kama wanda ake zargin wanda ya gudu tun ranar 6 ga watan Yuli.

Kakakin na NSCDC ya kuma bayyana cewa; Sashin leken asiri na rundunar ne suka cafke wanda ake zargin ne a ranar 13 ga Yuni bayan ya aikata laifin a Unguwar Shiyar Fara da ke karamar Hukumar Jega ta jihar, amma ya gudu.

Daga baya ne jami’an su suka kama shi a kan sa ido a ranar 6 ga Yuli kuma suka dawo da shi Birnin Kebbi.

Ya kara da cewa da zarar sun kammala hada bayanai game da lamarin zasu gurfanar da shi a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *