fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Jami’an Shige Da Fice Na Katsina Ba Su Iya Ko Fareti Ba>>Muhammad Babandede

Za mu tabbatar kowacce karamar hukuma a Nijeriya ta samu gurabe a daukar aikin da mu ke yi a halin yanzu.

 

Shugaban Hukumar Shige ta Fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya ce zai sauya wa jami’anta dake aiki a Katsina wuraren aiki, saboda yawan karbar rashawa.

Muhammad Babandede, wanda ya ziyarci jihar ranar Litinin, a wata ziyara ta kwana ukku, ya ce jami’an na jihar ba su iya ko fareti ba, amma har masauki suke bin bakin haure su karbi cin hanci.

“Yawancin ku kun ma san inda bakin hauren suke, kuna zuwa wurinsu ku karbi kudi; To a hir dinku! Saboda haka zan sauya wa mafi yawancin ku wuraren aiki nan gaba kadan.

Babadede ya kara da cewa “Na lura dadewar da mafi yawancin ku suka yi a nan fiye da kima ce ta haifar da wannan matsalar,”

Lokacin da yake jawabin ga jami’an dake aiki a jihar katsina, Babandede ya nuna fushinsa kan rashin iya faretinsu, amma, “Na sha samun rahoto kan shingayen binciken da kuke karbar kudade.

“Ban san wa kuke ba wa kudaden ba, domin dai a Abuja ban taba sanin ana tura kudade daga nan ba.

“Zan bincika, shin Kodinetan Shiyya ne ko Konturola-Konturola ne suke amsar kudaden. Idan (a cikinsu) da mai ba ku umarnin karbar kudade ku yi bayani.”

Kwanturola-Janar din ya kara da cewa duk jami’in da aka sauya wa wurin aiki daga Katsina ya nemi kamun kafa, to a bakin aikinsa.

“Na san me ke faruwa, amma tunda na sha yi muku magana na kuma ba da umarni kun yi kunnen kashi, to zan sauya muku wuraren aiki, ku je ku yi kamun kafa.

“Na san wadansunku za su je wurin wasu manya su roka cewa kar a sauya musu wurarin aiki. To duk wanda ya yi haka to a bakin aikinsa.”

Ya ce ya ziyarci Jihar Katsina ce domin aiki tare da sarakunan gargajiya wajen gano bakin haure a wani bangare na rage matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

“Matsalar tsaro a kasar nan ta yi yawa, shi ya sa na zo Katsina domin aiki tare da sarakunan gargajiya wajen zakulo bakin haure a lokacin da suke shigowa da kuma wadanda suke zama a Najeriya.

“Hakan ba zai yiwu ba muddin ku ma’aikatana ba ku da da’a, kuna karbar cin hanci ko ‘haraji’ a hannun mutane a kan iyakoki.

“Ba za ta sabu ba, kasarmu ba za ta ci gaba ba muddin muka mayar da rashawa wani bangare na rayuwarmu.

“Sai mun kawar da ita za mu samu nasara, amma kuma ban ga alamar da’a a tare da ku ba,” inji shi.

Jihar Katsina daya ce daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da matsalar tsaro ta ’yan bindiga ta fi ci wa tuwo a kwarya.

Muhammad Babandede ya ci gaba da cewa hukumar na ci gaba da daukar maaikata a halin yanzu domin magance matsalar karancin Ma’aikatan da hukumar ke fama da ita. Kuma za mu tabbatar kowacce karamar hukuma a Najeriya ta samu wakilci a wannan daukar aiki da mu ke yi.

Jiya ya kai ziyara a fadar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, inda ya tattauna hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro a jihar Katsina, da masu rike da sarautun gargajiya na Katsina. Haka kuma Shugaban Hukumar Shige Da Fice Na Najeriya ya kai ziyara a kan iyaka ta garin Jibia, inda ya tattauna da jamiansa dake aiki a wurin. Ana sa ran yau zai kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *