fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Jami’an tsaro sun dakile Yunkurin Satar Dalibai a Kaduna

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun sanar da dakile yunkurin ‘yan Bindiga na sace dibai a Kujama dake karamar hukumar Chukun.

 

Aun bayyana cewa, sun samu bayanan sirri ne kan satar daliban inda kuma suka garzaya wajan suka dakile harin.

 

Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar, Samuel Aruwan ya bayyana haka inda yace, da ‘yan Bindigar suka ji zuwa jami’an tsaro sai suka tsere suka tarehanyar Katari zuwa Tashan Ice, yace sun harbi mutane 3 sannan suka sace 2 amma an kwato su.

 

Yace ‘yan Bindigar sun kuma tare hanyar Zaria zuwa Kano wadda shima aka dakile harin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *