fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Jami’an tsaron dake yaki da ‘yan Bindiga sun koka da rashin biyan Alawus

Wasu jami’an tsaro na ‘yan sanda a Najeriya , da yanzu haka ke gudanar da aiki a cikin dazukan jihar Zamfara da ke yankin arewa masu yammacin kasar, sun koka da rashin samun kundaden alawus da ake basu.

Jami’an tsaron sunyi zargin cewa sun shafe watanni takwas ba tare da an basu wannan kudin alawus din ba.

Daya daga cikin jami’an ‘yan sandan da suka yi korafin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya suna cikin ka-ka-ni-kayi a Zamfara a yanzu.

Ya ce,” Mu dai gamu an jibge mu muna fama, muna wahala sannan kuma muna kwana idonmu biyu ba bacci, gaskiya hakkinmu ba a bamu, domin ba abamu abinci ko ruwan sha ballantana kudin alawus din daya kamata ace ana bamu”.

Dan sandan yace, baya ga wannan hali da suke ciki, ga kuma ‘yan bindiga ma ba su kyale su ba.

Jami’in dan sandan ya ce,” An zo an jibge mu a cikin daji wata takwas ba bu alawus, to ta ya ya zamu ji dadin aiki?”.

Ya ce, sai da tura ta kai bango ne sannan aka dauki naira dubu ashirin aka ba mu, to amma mu da muke daji ba bu abin da muka gani, in ji dan sandan.

Ya ce, ” Muna kawo kukanmu ga gwmanatin tarayya da ta jiha a kan a taimaka mana a bamu alawus din mu ko ma samu karsashi a aikin da muke yi”.

Jami’in dan sandan ya ce idan wata lalura ta samu daya daga ckinsu su da suke aiki a daji, to sai dai su hada kudi a junansu su taimaka wa mutumin.

Ya ce, a cikin albashinsu suke wannan taimakekeniya, amma, batun alawus kam sam ba bu shi don ba su gani ba a kasa.

To sai dai kuma a nata bangaren, gwamnatin jihar Zamfara ta tsame kanta daga cikin maganar cewa jami’an tsaro na ‘yan sanda a jihar ba sa samun kudin su na alawus har na tsawon watanni takwas kamar yadda wasu ke zargi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara, ya shaida wa BBC cewa, gwamnatin jiharsu ita take biyansu alawus a kowanne wata.

Ya ce a bisa tsarin duk dan sandan zai fita aiki a kowacce rana to yana da dubu guda, idan aka hada a kowanne wata alawus din kowanne dan sanda zai kasance dubu talatin ke nan.

Ibrahim Dosara, ya ce,” Muna da shaidar cewa an bawa kowanne dan sanda da ya yi aiki a Zamfara alawus din sa, domin duk wanda aka bai wa kudin, sai ya sanya hannu a kan takarda”.

Kwamishinan ya ce, hukumar ‘yan sanda ake ba wa kudin ta bayar, kuma ta tabbatar da an ba su, don haka batun cewa ‘yan sandan sun shafe wata takwas ba bu kudin alawus wannan ba gaskiya ba ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *