fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe yan bindiga 10 a Kaduna

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 10 a kusa da Fatika da ke karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Hakama rahotanni sun ce wasu maharan sun jikkata a musayar wuta da jami’an tsaron.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da aka yi garkuwa da shi.

Aruwan ya kara da cewa ‘yan bindigar da suka tsere sun bar mashunan su da wata babbar bindiga da wayoyi da fitilu da kuma layu.

Ya kuma shaida cewa an kona wasu daga cikin wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *