fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Jami’ar sufurin jiragen sama ta Najeriya ta samu amincewa, zata fara aiki a watan Yuli – Hadi Sirika

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya gabatar da takardar bayani game da jami’ar jirgin sama da sararin samaniya ta farko a Najeriya, kamar yadda aka ba da izini na wucin gadi don fara cibiyar.

Hakanan, Babban Sakatare, Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rashee, wanda ya karbi takardar bayanin daga Sirika a Abuja, ya sanar cewa jami’ar za ta kasance a karshen wannan watan.

Rasheed ya nakalto ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya, James Oduadu ya fitar a ranar Juma’a yana cewa, “Ina baku tabbacin zuwa karshen wata (Yuli), za mu samu sabuwar jami’a; irinsa na farko a Abuja, jami’ar Afirka ta farko da aka sadaukar domin nazarin tukin jirgin sama da sararin samaniya a kasar. ”

Shugaban NUC din ya tabbatar wa da Ministan Sufurin Jiragen saman cewa hukumar za ta hada kai da wasu farfesoshin da za su kammala bayanin yadda za a amince da ita nan take, saboda ya jaddada cewa ba za a iya kirga darajar irin wannan jami’ar ba.

Rasheed ya ce, “Jirgin sama a karkashin jagorancin ka (Sirika) zai kasance na farko da zai nuna mana hanyar da za mu tallafa wajen kafa jami’a ta musamman wacce ba za ta yi mana aiki ba kawai amma za ta yi aiki ga yankin Afirka da kuma kasashen duniya,” in ji shi.

Sirika, wanda ya samu rakiyar NUC tare da babban sakataren din-din-din na ma’aikatar jirgin sama, daraktoci da shugabannin hukumomi, ya ce sunan cibiyar ita ce Jami’ar Sufurin Jiragen Sama da sararin samaniya, wato aviation and aerospace university Abuja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *