fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Jam’iyyar APC reshen Jihar Bauchi ta ki karba kayan azumi daga Gwamna Bala Mohammed

Jam’iyyar All Progressive Congress, APC reshen jihar Bauchi ta yi watsi da kayayyakin abinci da Gwamna Bala Mohammed ya bayar don tallafawa marasa karfi a azumin watan Ramadan.

Kayan abincin, sun hada da shinkafa, masara, dawa, taliya spaghetti da sukari.

An kai kayayyakin ga Sakataren jam’iyyar a ranar Laraba amma jami’an jam’iyyar suka ki amincewa da karba kayan.

Da yake magana da manema labarai, Sakataren yada labarai na APC, Adamu Aliyu-Jallah, ya ce, ya saba wa al’adar APC a karbi kayan tallafi daga PDP.

Mista Aliyu-Jallah ya ce: A matsayinsu na kwamatin aiki na reshen APC sun ki amincewa da karba kayan saboda matsalar ita ce idan suka karba, hakan zai iya janyo masu kananan maganganu.

Abu na biyu shi ne, a azumin Ramadan shekarar da ta gabata, PDP bata aiko mana komai ba, me yasa yanzu suka aiko mana?

Bayan wannan, akwai ma’aikatan da har yanzu ba a biya su albashin su ba, su ya kamata a baiwa wannan tallafin bamu ba.

Don haka ba za mu iya karbar komai daga wata jam’iyya adawa ba ba, saboda haka babu wani dalili da zai sa a aiko mana wani abu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *