fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Jam’iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi na Jigawa

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammad Adamu, ya zama wanda ya lashe zaben cike gurbi na Mazabar Kafinhausa na ranar Asabar a Jigawa.
Adamu ya samu kuri’u 14,924 domin kayar da sauran ‘yan takarar a zaben.
NAN ta ruwaito cewa an gudanar da zaben a rumfunan zabe 120 a yankin.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ahmed Kutama ne ya bayyana sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaben a karamar hukumar Kafinhausa.
Ya ce dan takarar na APC ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Garba Muhammad Tambale, na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu kuri’u 8,612.
Jami’in zaben ya bayyana Adamu a matsayin wanda ya lashe, bayan da ya samu kuri’u mafi yawa.
Wanda ya zo na uku shi ne Usman Isyako na Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) wanda ya samu kuri’u 72.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *