fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Jam’iyyar APC ta lashe zaben kujerun Ciyamomi dana Kansiloli a Jihar Filato

Hukumar zabe mai zaman kanta a reshen Jihar Filato ta ayyana Jam’iyyar All Progressive Congress, APC a mtasayin wadda ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi da kansiloli a kananan hukumomi 17 na jihar.

Fabian Ntung, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Filato, PLASIEC, ya sanar da sakamakon a ranar Lahadi a Jos.

Mista Ntung ya yi bayanin cewa APC ta lashe dukkan kujerun kansiloli 325 a cikin kananan hukumomi 17, kuma hukumar ta gamsu da yadda aka gudanar da zaben.

Mista Ntung ya yabawa masu kada kuri’a wadanda suka tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Hukumar dai ta hana jam’iyyar adawa ta PDP shiga zaben, sakamakon wasu rikice -rikicen cikin gida.

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci cire zaben, inda ta saka kara a Babbar Kotun da Kotun daukaka kara, amma duk da hakan ba su yi nasara ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *