fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Jam’iyyar APC za ta yi duk abin da za ta iya domin karbe kujerar Gwamna ta jihar Anambra, a zabe mai zuwa – Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta yi duk abin da za ta yi domin karbe kujerar Gwamna a zabe mai zuwa da aka shirya gudanarwa a Jihar Anambra, a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2020.

Chris Ngige wanda shi tsohon Gwamnan jihar Anambra ne, ya fadi hakan a karshen mako yayin wani taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da mambobin kwamitin rajista da sake sauya sheka a Awka, babban birnin jihar, ya bayyana cewa gwamnatin All Progressive Grand Alliance (APGA) a jihar ta gaza samar da shugabanci na gari ga mutanen Jihar.

Ngige ya kuma ce, kyakkyawan shugabanci a Jihar ya kare a 2006 lokacin da ya bar mulki, sannan ya kara da cewa APC za ta nada Gwamna wanda zai ci gaba daga inda ya tsaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *