fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Jam’iyyu 18 da suka tsallake siradin tantancewar INEC

A ranar Alhamis ne hukumar Zabe ta kasa me zaman kanta ta soke rijistar wasu jam’iyyu 74 bisa kasa cika sharudan da doka ta tanda da suka yi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyanawa manema labarai a Abùja cewa jam’iyyun da aka sake lasisin nasu sun kasa cika dokar da kundin tsarin mulki ya tana da na samun akalla kaso 25 cikin 100 na kuri’un zaben shugaban kasa a jiya a kalla 1.

Ko kuma samun kaso 25 na Kuri’un da aka kada a karamar hukuma 1 da kuma kasa cin zabe a mazaba daya a zaben kananan hukumomi, Kujera daya a majalisar jiha ko ta kasa ko kuma cin zaben koda kansila daya ne.

A karshen wannan tantancewa jam’iyyu 18 ne kacal suka tsallake siradi wanda sune:

1. Accord Party A
2. Action Alliance AA
3. African Action Congress AAC
4. African Democratic Congress ADC
5. African Democratic Party ADP
6. All Progressives Congress APC
7. All Progressives Grand Alliance APGA
8. Allied Peoples Movement APM
9. Labour Party LP
10. New Nigeria Peoples Party NNPP
11. National Rescue Movement NRM
12. Peoples Democratic Party PDP
13. Peoples Redemption Party PRP
14. Social Democratic Party SDP
15. Young Progressive Party YPP
16. Zenith Labour Party ZLP
17. Action Peoples Party APP
18. Boot Party BT


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *