fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Jam’iyyun Hamayya Masu neman shugabancin Najeriya s 2023 su manta, ‘Yan Najeriya ba zasu taba juyawa shugaba Buhari baya ba>>Garba Shehu

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ‘yan Jam’iyyar Hamayya masu neman shugabancin Najeriya a 2023 su manta dan kuwa ‘yan Najeriya ba zasu taba juyawa Gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari baya ba.

 

Ya bayyana hakane bayan Sallar Ido inda hake magana kan irin tarbar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu a Mahaifarsa, Daura.

 

Garba yace, ai wannan soyayya ba a daura bane kawai, gaba dayan kasar ba zasu juyawa APC da shugaba Buhari baya ba.

 

Saidai kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa, wannan labarine, dan kuwa ba zasu amince da hakan ba.

 

Yace wannan na nuni da alamar zargin da mutane da yawa suke na cewa, shugaba Buhari na son yiwa ‘yan Najeriyar karfa-karfa ta hanyar nada musu magaji idan zai sauka daga Mulki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *