fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Janar din soja ya tsallake rijiya da baya a hannun Boko Haram

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Janar Olusegun Adeniyi ya tsallake rijiya da baya bayan ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi kwantar bauna ga ayarin motocinsa a ranar Litinin a hanyar Jakana da ke jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani daga cikin sojojin kasar ya shaida musu cewa kwamandan yana hanyarsa ne ta komawa Maiduguri bayan wata ziyara da ya kai wa wasu dakarun da aka tura garin Jakana ba da dadewa ba.
An tura jami’an sojin ne zuwa Jakana domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin daga Boko Haram.
An ruwaito cewa motar da kwamandan yake ciki ta sha ruwan harsasai wanda hakan ya sa motar ta yi kaca-kaca.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *