fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ji dalildai masu kwari dake nuni da Gwamna Ganduje ne zai zama Mataimakin shugaban kasa idan APC taci zabe a 2023

A yayin da ake fuskantar karatowar zaben shekarar 2023, Jam’iyyar APC ana tsammanin zata fitar da dan takararta daga kudancin Najeriya ne.

 

Ana tunanin, Fashola, Tinubu, Osibajo, Kalu da sauransu ne ka iya zama ‘yan takarar jam’iyyar.

 

Tuni dai Tinubu ya bayyana karara cewa shine kan gaba wajan son zama shugaban kasa a shekarar 2023, kamar yanda hutudole.com ta fahimta.

 

Amma saidai bai fito da kansa ya bayyana hakan ba, saidai ana ta samun karuwar kungiyoyin dake mara masa baya kan ya tsaya takarar shugaban kasar.

 

Koda a baya, lokacin da yayi jinya a kasar Ingila, yayin da wasu ‘yan majalisa suka je masa jaje, hutudole.com ya ruwaito muku yanda wani daga cikin ‘yan majalisar ya rika kiran Tinubu da shugaban kasa.

 

A yayin da Tinubu ke shirin zama shugaban kasa, idan hakan ta tabbata, to Alamu sun nuna sosai cewa, Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne zai zamar masa Mataimakin shugaban kasa.

 

Kano na daga cikin manya-manyan jihohin da kowane dan takarar shugaban kasa yake son ci, kuma jihohin dake kawo mafiya yawan kuri’u a Arewa suna Arewa maso yamma ne.

 

Watau Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi.

 

Idan aka duba tarihi, yawanci Kano na jagorantar sauran jihohin Arewa akan zaben shugaban kasa ta yanda duk wanda ya samu nasarar jama’ar Kano to kamar ya samu Nasarar jama’ar Arewa baki daya ne.

 

Gwamna Ganduje Tuni shima ya fara ziyarce-ziyarce musamman zuwa kudancin Najeriya wajan manya-manyan tarukan gargajiya dana siyasa, wanda duk wannan alamu ne dake nhna cewa dashi za’a yi tafiyar shekarar 2023.

 

Hakanan shima Tinubu, a yanzu, ya fi mayar da hankali a Kano fiye da sauran jihohin Arewa.

 

Koda a baya dai an ga wasu fastocin Mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo da Gwamna Ganduje a matsayin Mataimakin sa na takarar shugaban kasa.

 

Saidai masu iya magana na cewa,  ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *