fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ji gagarumar nasarar kisan Gwamman ‘yan Boko Haram da Sojojin Najeriya suka samu

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce ta yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram sama da 38 ciki har da sabon shugaban kungiyar ISWAP wanda ake kira Mallam Bako.

Hukumomin tsaron sun ce sun samu wannan nasara ce a hare-haren da suka rika kaiwa ta sama da ta kasa a cikin mako biyu a karkashin shirin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabas.

Sojin sun kuma ce hare-haren sun sa mayakan Boko Haram da iyalansu sama da dubu daya sun mika wuya a tsawon wannan lokaci.

A wata hira da BBC wani jami’i a sashen hulda da ‘yan jarida na shelkwatar tsaron, Kawamanda AbdulSalam Sani ya ce, sojojin na samun nasara a yankin arewa maso yamma a yaki da barayin daji.

Daga cikin nasarorin, sojojin sun ce sun hallaka barayin daji sama da 70, kuma sama da 50 daga cikinsu a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna ne.

Sauran kuwa a sassan jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kebbi ne, kamar yadda sojojin suka ce.

Sai dai kuma babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na sojojin na Najeriya.

Har yanzu dai akan samu hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kaiwa a sassan arewa maso gabashin Najeriyar, yayin da su kuma ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar wasu sassan arewa maso yammacin kasar, duk da nasarar da hukumomin kasar ke cewa suna samu a kansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *